Gwamnatin tarayya tana so mu shiga yajin aiki-ASUU

asuu
asuu

Kungiyar malaman jami’o’I ta kasa ASUU ta jadadda cewa har yanzu bata ji wani bayani daga gwamnatin tarayya ba dangane da bukatun da suke nema a biya musu.

Babban jami’in dake kula da shiyyar Abuja Dakta Salahu Lawal ne ya bayyana hakan a wajen taron manema labarai da ya gudanar yau a Abuja.

Ya ce shiru da gwamnatin tarayya ta yi da kin martaba yarjejeniyar da suka yi a watan disamban shekarar 2020 yana nuna cewa gwamnati so take su shigan yajin aiki.

Dakta Salahu Lawal ya kara da cewa basu ji dadin abunda gwamnatin tarayya ta yi ba na sanya hannu kan yarjejeniya, sannan taki aiwatar da abunda yarjejeniyar ta kunsa.

Ya tabbatar da cewa matukar gwamnatin tarayya bata aiwatar da wannan yarjejeniya ba to babu abunda zai hana su shiga yajin aiki, yana mai cewa aiwatar da wannan yarjejeniya zai taimaka wajen kawo gagarumin gyara kan tsarin koyo da koyarwa a jami’o’in Nigeria.

Dakta Salahu Lawal  ya yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki dasu sanya baki kan wannan Magana domin kaucewa shiga yajin aiki da kungiyar ta shirya yi.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here