Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’a (JAMB) ta ce za a fara jarrabawar shiga jami’a ta 2025 (UTME) a ranar 24 ga Afrilu ba 25 ga Afrilu ba kamar yadda ta sanar a baya.
Mai magana da yawun hukumar ta JAMB, Dr Fabian Benjamin ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Asabar.
Benjamin ya ce an yi wannan gyara ne domin cika muhimman alkawurran da hukumar ta yi da hukumomin hadin gwiwa.
Ya ce a yanzu masu son shiga za su iya buga takardun sanarwar su, wadanda ke dauke da muhimman bayanai dangane da bayanan jarrabawar su.
Ya kara da cewa takardar sanarwar ta nuna ranar jarrabawar, wurin (cibiyar), lokaci da sauran muhimman bayanai da suka dace don samun nasarar jarrabawar.
Karin karatu: Gidauniyar Barau ta tantance ɗalibai 215 don ba su tallafin karatu a gida na shekarar 2025
Ya shawarci dalibai da su san wuraren da za su gudanar da jarrabawar bayan sun buga takardunsu, akalla kwana daya ko biyu kafin ranar da za a gudanar da jarrabawar.
A cewarsa, wannan shiri zai taimaka wajen tabbatar da samun sauki a ranar jarrabawar.
Benjamin ya ci gaba da cewa, za a ba wa dalibai cibiyoyi ne a garuruwan da suka zaba domin yin jarrabawa. (NAN)