JAMB ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan sama wa ɗaliban da shekarun su ba su kai ba guraben Karatu

Jamb 1 2

A yau Laraba ne Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare ta Najeriya JAMB ta kaddamar da wani kwamiti da zai yi nazari kan yadda za a gudanar da jarabawar ga daliban da shekarunsu ba su isa shiga jami’a ba a hukumance.

Shugaban hukumar ta JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, ne ya bayyana haka a wajen taron kaddamar da mambobin kwamitin a Bwari, babban birnin tarayya Abuja.

“Waɗannan su ne dalibai 599 da shekarunsu ba su karasa ba amma suka samu maki 320 da sama da haka a jarabawar UTME ta bana.

“Kwamitin zai yanke shawara kan ranakun da abin da zai yi da kuma kafa wadanda za su zaba a karshe, za su zabo hazikan dalibai da za a basu damar shiga manyan makarantu domin karfafa musu gwiwa,” inji shi.

Shugaban na JAMB ya bayyana cewa taron kwamitin ya samu halartar shugabannin jami’o’in Najeriya da hukumomin da suka dace da wasu masu ruwa da tsaki da kwararru a fannin ilimi.

Ya kara da cewa, kwamitin ya yanke shawarar cewa daga yanzu zuwa watan Satumba, za a bayyana wadanda za su samu nasara cikin dalibai 599.

“Duk daliin da ya samu kasa da maki 80 a jarrabawar Post-UTME to ba zai kasance cikin masu nasara ba.

Ya kara da cewa kwamitin zai zauna a Legas da Abuja da kuma Owerri.

Oloyede ya bukaci iyaye da su kau da kai daga matsananciyar damuwa su damu da ilimin ‘ya’yansu a lokacin da suke kanana har ma zuwa lokacin da za su shiga manyan makarantu, yana mai cewa yara na bukatar lokaci don bunkasa dabi’a har zuwa girmansu.

Shugaban na hukumar JAMB, ya tabbatar da cewa tsarin shigar da daliban zai kasance cikin gaskiya da adalci saboda ingancin mambobin kwamitin.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here