NSCDC ta cafke wanda ake zargi da Dillancin Ƙwayoyi da kuma waɗan ke fasa gidaje

NSCDC NSCDC

Hukumar Tsaro ta Civil Defense shiyyar Kano, ta ce, jami’anta sun cafke wasu mutane biyu da ake zarginsu da aikata laifuka daban-daban.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar SC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

Ya ce sun samu nasarar cafke mutanen ne a wani samame da suka kai a unguwar Salanta da ke karamar hukumar Gwale, inda suka kama Basiru Ahmed mai shekaru 42 da ake zarginsa da sayar da miyagun kwayoyi inda aka cafke shi da kunshi fiye da 106 na tabar wiwi da rahotonni suka bayyana cewa sayar da su ya ke yi.

Haka kuma SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya ce sun kama wani matashi Muhammad Abbas mai shekaru 22 a unguwar Gurungawa da ke karamar hukumar Kumbotso wanda ake zarginsa da fasa gidaje tare da sace kayayyaki na dubban Naira.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Civil Defense shiyyar Kano ya kara da cewar za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here