Fiye da fursunoni 37 da aka yankewa hukuncin kisa ne ke jiran aiwatar musu da kisa bayan yanke musu hukuncin manyan laifuka a jihar Bauchi.
Jami’in hulɗa da Jama’a na Hukumar kula da gidajen gyaran hali NCoS, reshen jihar ta Bauchi Ahmed Tata, ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a yau Talata a Bauchi.
Da ya ke mayar da martani ga binciken da NAN ta yi kan dalilin da ya sa gwamnonin jihohin ke ƙin sanya hannu kan zartar da kisan, Tata ya ce, fursunonin da aka yanke wa hukuncin sun haɗa da maza 36 da mace ɗaya.
Ya ƙara da cewa, babu wani daga cikin gwamnonin da aka zaɓa a jihar da ya rattaɓa hannu kan takardar hukuncin kisa tun shekarar 1999.
Sai dai jami’in ya ce, gwamnoni a lokacin sojoji sun rattaɓa hannu a kan zartar da kisa ga waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa.
Wani masanin fannin shari’a, Jubrin S. Jubrin, ya bukaci gwamnonin jihohi da su riƙa gaggauta sanya hannu kan zartar da hukuncin kashe fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisan don tabbatar da adalci.
Jubrin ya ce, abin da gwamnonin ke yi na iya kasancewa ya na da alaka da mugunyar fursunonin da aka yankewa hukunci a kasar.
Malam Garba Jinjiri, shugaban gamayyar hadin gwiwar kungiyoyin fararen hula CSOs a Bauchi, ya bayyana cewa rashin sauya hukuncin kisa na daya daga cikin dalilan da suka sa gwamnonin suka ki sanya hannu kan takardar kisa.













































