Gwamnonin jihohin Arewa suna taro a Kaduna

Northern governors
Northern governors

Gwamnonin jihohin Arewa 19 karkashin kungiyar gwamnonin Arewa suna taro yanzu haka a Kaduna.

Gwamnonin Arewa
Kungiyar Gwamnonin Arewa sun gudanar da taro

Gwamnonin dai na tattaunawa ne a kan rashin tsaro, noma, da hako mai a yankin arewa tare da jajanta wa gwamnan Kaduna game da harin da aka yi na Tudun Biri.

Taron da Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ke karabar bakuncinsa, shi ne na farko da suka yi tun bayan hawan su a watan Mayun 2023.

Karanta wannan: Sojoji sun hallaka yan bindiga a Sokoto

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda.

Sai kuma mataimakan gwamnonin jihohin Jigawa da Bauchi da Kano da Yobe, da Kwara, wadanda ke wakiltar gwamnonin jihohinsu.

Gwamnonin Arewa, Jihohin, jihohin
Gwamnonin Jihohin Arewa a yayin da suke taro a Kaduna

Karanta wannan: Wasu kwamishinonin biyu sun yi murabus daga majalisar zartarwar Fubara

Da yake jawabi Shugaban kungiyar, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai wa al’ummar Tudun Biri.

Yace akwai bukatar Gwamnonin yankin arewa su kara zage damtse wajen yaki da rashin tsaro da ke addabar al’umma.

Ya kara da cewa har yanzu magance matsalar rashin tsaro da sauran kalubale na da matukar muhimmanci ga ci gaban al’ummar yankin arewa.

A cewarsa kungiyar jagorancinsa, na aiki tukuru don ganin cewa an yi bincike sahihi kan lamarin da ya faru a Tudun Biri.

A jawabinsa a matsayin babban mai masaukin baki, Gwamnan Kaduna ya gode musu bisa yadda suka jajantawa jama’a kan asarar rayukan da aka samu a harin.

Gwamnan ya koka da yadda ake fama da matsalar rashin tsaro a arewa inda ya jaddada bukatar hadin kai a yankin arewa.

Gwamnan ya kuma ce yin watsi bambancin ra’ayi da kabilanci ya kasance ginshikin zaman lafiya da tsaro da ci gaban yankin Arewa.

Yace dole ne su hada kai wajen baiwa jama’a karfin gwiwa a matsayin jiga-jigan samar da ci gaban arewa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here