Rikicin da ya mamaye jihar Ribas na dada Kamari yayin da wasu kwamishinoni uku suka yi murabus daga majalisar zartarwar gwamna Sim Fubara.
Na baya-bayan nan da suka fice daga majalisar sun hada da kwamishinan ayyuka George-Kelly Alabo da takwararsa ta walwala da jin dadin jama’a Inime Aguma.
Murabus din nasu na zuwa ne bayan kwamishinan shari’a Farfesa Zacchaeus Adangor ya ajiye mukaminsa.
Karanta wannan:Kwamishinan shari’a na jihar Rivers ya ajiye aiki
Guguwar murabus din da ta dabaibaye majalisar zaratarwar Rivers, ita ce sabon salo a rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar mai arzikin man fetur tun bayan da aka fara takaddama tsakanin ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike da Fubara.
Tuni dai an samu baraka a Majalisar Dokokin Jihar Ribas ganin cewa majalisar mai wakilai 32 a yanzu tana da bangarori biyu.
A farkon makon nan ne ‘yan majalisar 27 ‘yan asalin jam’iyyar PDP suka sauya sheka zuwa APC.
Sai dai shugaban Majalisar Edison Ehie ya bayyana kujerunsu a matsayin wadanda ake da gyibin su a dalilin sauya shekar.