Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya je dakin taro na Banquet dake fadar shugaban kasa, Villa, Abuja, a ranar Litinin.
Jagoran Kwankwasiyyar ya halarci taron tattalin arzikin gandun daji na Najeriya na 2025, wanda kwamitin shugaban kasa kan tattalin arziki da hada-hadar kudi (PreCEFI) ya shirya.
Kamar yadda Aminiya ta ruwaito, Kwamlwaso bai gabatar da jawabi a wajen taron ba kuma bai yi magana da manema labarai a wajen taron ba.













































