Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Aminu Gidado Yusha’u a matsayin babban mai kula da shirin ayyukan raya kasa na Kano, Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL).
ACRESAL wani shiri ne na Bankin Duniya tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya da Jihohin Arewa 19, ciki har da FCT.
SolaceBase ta rahoto cewa nadin nasa ya biyo bayan daga likkafar tsohon shugaban shirin, Dr. Dahir M. Hashim, zuwa kwamishina a farkon wannan shekarar.
A cikin sakon taya murna da kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano, Dakta Dahir M. Hashim ya sanyawa hannu a ranar Talata, ya bayyana nadin Aminu Gidado Yusha’u a matsayin wanda ya cancanta.













































