Gwamnatin Kano Zata Biya Diyar Naira Biliyan Uku Ga masu Shagunan  Masallacin Eid 

Abba Kabir Yusuf Kano Governor 750x430
Abba Kabir Yusuf Kano Governor 750x430

A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta amince zata biya diyyar Naira biliyan 3 ga masu shuganan da ta rusa musu a masallacin Eidi, ba bisa ka’ida ba.

An cimma yarjejeniyar ne sakamakon wata takardar sasantawa da lauyoyin masu kara da da kuma na gwamnatin Kano, mai dauke da kwanan 12 ga watan Disamba, wacce kuma a aka gabatar da takardar a gaban ranar da 13 ga watan Disamba a gaban mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, biyo bayan rusa shagunan da Gwamna Abba Yusuf ya yi, mutane 56 sun shigar da gwamnatin ta Kano kara a madadin kungiyoyin yan kasuwa na masallacin Idi, wacce  karar ke da lamba FHC/KN/CS/208/2023.

Yan kasuwar sun shigar da gwamnatin Kano, hukumar tsara birane ta jihar Kano; babban lauyan gwamnati, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano; Kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya; da kukma NSCDC ta Jihar Kano.

A Tun a baya mai shari’a Samuel Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano, a ranar 29 ga watan Satumba ya umarci gwamnatin jihar da ta biya ‘yan kasuwar naira biliyan 30 a matsayin diyya, sakamakon lalata musu kadarorin su da gwamnatin tayi ba bisa ka’ida ba.

Amma sakamakon kin bin umarnin kotun da gwamnatin jihar ta yi, ‘yan kasuwar sun kara shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1382/2023 a gaban mai shari’a Ekwo, domin cigaba da neman hakin su.

Sai dai kuma da aka ci gaba da sauraren karar a ranar Alhamis, lauyan masu  ya shaida wa kotun cewa bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya.

“Muna farin cikin sanar da kotu cewa masu kara da wadan da ake kara sun cimma matsaya. A kan haka ne muka gabatar da sharuddan sasantawa.”

Layoyin duka bangarorin biyu sun amince da sharuddan sasantawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here