Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da aikin duban tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025 domin baiwa daliban da za su rubuta jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan JAMB damar isa cibiyoyin jarrabawar a kan lokaci.
Kwamishinan muhalli da kula da sauyin yanayi Dakta Dahir Hashim Muhammad ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Sama’ila Garba Gwammaja ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce, an dauki wannan matakin ne bayan nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki, a kokarinta baiwa daliban jihar Kano damar rubuta jarabawarsu ba tare da wata matsala ba.
Dr. Dahiru Hashim Muhammad ya tabbatar wa mazauna Kano cewa dakatarwar na wucin gadi ne a wannan watan kawai, kuma za a ci gaba da aikin tsaftar mahalli a watan Mayun 2025.
Kwamishinan ya yi kira ga mazauna garin da su ba hukuma hadin kai da fahimtar dalilin da ya sa aka yanke wannan hukunci musamman na ganin cewa ayyukan tsaftar muhalli ba su ci karo da wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a jihar ba.
“Dakatar da aka yi na da nufin hana duk wata matsala da za ta iya kawo cikas ga aikin jarrabawar da kuma tabbatar da cewa dalibai za su iya rubuta jarabawarsu ba tare da wani shamaki ba, in ji Kwamishinan.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin yanayi Dr. Dahiru M. Hashim ya tabbatar wa mazauna yankin cewa dakatarwar na wucin gadi ne na watan Afrilu kawai, kuma za a ci gaba da aikin tsaftar mahalli a watan Mayu 2025, a jihar
Kwamishinan ya yi kira ga mazauna garin da su ba hukuma hadin kai da fahimtar dalilin da ya sa aka yanke wannan hukunci. “Mun himmatu wajen tabbatar da tsafta da lafiya, kuma za mu yi aiki tukuru don ganin cewa ayyukan tsaftar muhalli ba su ci karo da wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a jihar ba”.
Da yake yabawa mazauna yankin bisa fahimtarsu da hadin kan da suke baiwa wannan gwamnati, ya bukace su da su ci gaba da gujewa zubar da sharar gida barkatai, tare da ba ma’aikatan tsaftar muhalli hadin kai domin tabbatar da tsaftar muhalli a kodayaushe.