Babban bankin kasa CBN ya amince da baiwa maniyyata aikin hajjin 2025 kudin guzurinsu a hannu, bayan da bankin ya amince da bukatar gwamnatin tarayya na bayar da kudaden a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki.
Hakan ya biyo bayan tsoma bakin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya roki shugaban kasa Bola Tinubu a madadin maniyyatan ta hannun hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), kamar yadda wata sanarwa daga ofishinsa ta tabbatar.
“An bayyana damuwa game da tsarin da CBN ya sharɗanta na kowane mahajjaci ya yi amfani da katin banki a matsayin wanda zai iya kawo tarnaƙi ga tsari da aikin gudanar da Hajjin 2025,” in ji sanarwar da Stanley Nkwocha ya fitar.
Sanarwar ta ambato kwamashinan tsare-tsare da ayyukan kuɗi na hukumar alhazai, Aliu Abdulrazaq, na cewa hakan zai bai wa mahajjan Najeriya damar kashe da hannunsu yayin ibadar a Saudiyya.
“Tun kafin yanzu mun sha yin ganawa game da kuɗin guziri a aikin Hajjin na 2025. Daga baya mataimakin shugaban ƙasa ya shiga lamarin kuma ya nemi alfarmar CBN,” a cewar kwamashinan.
Karanta: Hajj 2025: NAHCON da hukumar jin dadin alhazai ta jiha sun tsayar da ranar fara jigilar Maniyyata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa, a farkon wannan shekarar ne CBN ya bullo da wata sabuwar hanyar biyan kudin guzuri wato basic Travel Allowance (BTA) ga ‘yan Najeriya masu zuwa aikin hajjin 2025.
Da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawa da mataimakin shugaban kasa, kwamishinan kula da ma’aikata da kudi na NAHCON, Aliu Abdulrazaq, ya tabbatar da cewa bankin na CBN ya baiwa alhazan Najeriya damar yin hada-hadar kudi don gudanar da aikin hajji mai zuwa.
A cewar Abdulrazaq, taron ya biyo bayan manufofin gwamnatin tarayya kan katin ba da izinin tafiya aikin Hajji na shekarar 2025 (BTA).
Daga cikin martabar babban bankin CBN da roko da mataimakin shugaban kasar ya yi, an yi watsi da tunanin katin da za a yi wa maniyyata aikin hajjin 2025.
“Wannan babbar nasara ce ga hukumar NAHCON, idan ka je Saudiyya galibi wuraren da alhazai za su gudanar da ibadarsu, akwai Injin ATM.
“Kuma koyaushe yana cike da cunkoso kuma yana haifar da matsaloli masu yawa ga mahajjata don siyan duk abin da suke so.”
“Amma yanzu muna da yakinin cewa ayyukan Hajji ba za su yi wa maniyyata cikas ba, domin duk shirye-shirye sun yi nisa, hatta BTA da muke tsoro yanzu an magance ta.”
Hakazalika, Sakataren Hukumar ta NAHCON, Dskta Mustapha Ali, ya bayyana cewa sauya tsarin ba wani rangwame ba ne ko tallafi daga Gwamnatin Tarayya.
“Akwai bukatar a yi karin haske, ba rangwame ko sa hannun gwamnatin tarayya ba ne, ba tallafi ba ne.
“Mataimakin shugaban kasar ya shiga tsakani ne saboda galibin mahajjata na yin sayayya a titunan Makka ko Madina, kuma ba sa bukatar katin ciro kudi don yin sayayyar.
Yanzu an ba su izinin ɗaukar kuɗi. Babban bankin na CBN zai samar da kudin a kan farashin kasuwa,”.
Hakazalika, Malam Abba Aliyu, Daraktan Ma’aikata na CBN kuma mamba mai wakiltar CBN a NAHCON, ya bayyana cewa babban bankin ya dauki matakin ne domin jin dadin alhazan Najeriya.
“Idan muka dubi yadda alhazai suke da bukatar kudi, akwai bukatar mu saukaka musu rayuwa domin da yawa daga cikinsu ba su san yadda ake sarrafa na’urar ATM ba,” inji shi. (NAN)