Rundunar sojin saman Najeriya ta ce za ta tabbatar da gudanar da cikakken bincike kan musabbabin hatsarin jirginta Super Mushshak da ya yi hatsari jiya Talata a sansaninta da ke Kaduna.
Daraktan hulɗa da jama’a da yada labarai na shalkwatar so jin saman Air Commodore Edward Gabkwwt ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da yammacin yau Laraba a Abuja.
A cewarsa, babban hafsan sojin sama Air Marshal Oladayo Amao, ne ya bayyana aniyar binciken lokacin da ya ziyarci iyalai da abokan aikin matuƙan jirgi biyu da suka rasa rayukansu a hatsarin wanda ya rutsa da jami’an Flt. Abubakar Alkali da Flt. Lt. Iliya Karatu.
Sai dai Amao ya kafa kwamitin binciken kan lamarin bayan da ya samu labarin faruwar hatsarin domin sanin musabbabinsa.
Shugaban rundunar soji saman, ya kuma bai wa jami’an makarantar horaswa kan tuƙin jiragen sama ta 401 Flying Training School da ke Kaduna cewa za a yi amfani da dukkan matakan da suka dace don dakile afkuwar irin wannan hatsari a gaba.
Ya kuma tunatar da su kan buƙatar su tsaya tsayin daka tare da mayar da hankali kan ayyukan da aka ɗora musu bisa la’akari da babban aikin da ke gaban rundunar soji saman da sauran hukumomin tsaro.
Ya ce hakan ne ya sa su ci gaba da kawar da yankin Arewa maso Yamma da ma ɗaukacin al’ummar Najeriya daga duk wani abu da ya shafi miyagun laifuka.













































