Wasu ƴan ta’adda da ake kyautata zaton ƴan kungiyar tada ƙayar baya ta ISWAP ne ko kuma mambobin Boko Haram, sun kashe mutane da dama waɗanda suka fita yawon shaƙatawa a karamar hukumar Gaidam da ke jihar Yobe.
PRNigeria ta ruwaito cewa, ƴan ta’addar sun kutsa kai ne cikin garin inda kuma suka afka wurin wanda ake sayar da barasa da naman kare.
A ƙoƙarin da ƴan ta’addan suka yi na kauce wa daukar hankalin sojoji, sun ɗaure waɗanda lamarin ya ritsa da su tare da yayyanka su da wukake masu kaifi.
Guda daga cikin majiyoyi ta shaida wa PRNigeria cewa wasu daga cikin waɗanda aka hallaka ɓata garin sun yanke musu kawuna tare da ɗorawa a kan gangar jikinsu.
Ka zalika sun ajiye baburansu ne a wata unguwa da ke makwabtaka da wurin.
Rahotonni sun ce, ƴan ta’addar sun shiga ta gabashin garin inda suka ƙona makarantar kimiyya da fasaha ta gwamnati da ke garin na Geidam, tare da kashe mutum ɗaya a harabar makarantar.
Wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta ta ce ƴan bindigar sun kuma kai hari wani babban gidan karuwai a garin na Geidam, inda suka yi wa mutane 10 yankan rago waɗanda suka haɗa maza da mata.
“Sun ba mu mamaki a wannan karon; sun shiga shiru ba tare da harbin bindiga ko amfani da ababen hawa ba.”
“Da shigarsu, sai suka nemi wasu daga cikin mazauna garin da su karanta ayoyin Alkur’ani kafin su bar su su fita ko kuma a kashe su.”













































