Shugabannin APC sun gudanar da ganawar sirri da gwamnan Bauchi, kwana guda bayan ziyarar ADC a jihar

Yilwatda Mohammed and Yusuf in Bauchi on Wednesday April 1 2026

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya gudanar da wata ganawa ta sirri da shugabannin jam’iyyar APC na ƙasa a ranar Laraba a gidan gwamnati da ke Bauchi.

Tawagar ta haɗa da shugaban APC na ƙasa Nentawe Yilwatda da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane uku kacal suka halarci ganawar, domin sauran mambobin shugabannin jam’iyyar a jihar ba a ba su damar shiga ba.

Haka kuma an hana kafafen yaɗa labarai damar daukar rahoto.

Gwamna Mohammed da Nentawe Yilwatda sun ƙi yin magana da manema labarai, inda suka bayyana ziyarar a matsayin ta sirri.

Ganawar ta zo ne kwana guda bayan gwamnan ya nuna sha’awar shiga jam’iyyar ADC, bayan wata ziyara da tawagar jam’iyyar ta kai masa a Bauchi.

Tawagar ADC ɗin ta samu jagorancin tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal yayin ziyarar da ta gudana a jihar Bauchi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here