Rikici ya barke a Jos a ranar Laraba, sa’o’i kadan bayan gwamnatin jihar Filato ta sassauta dokar hana fita da ta sanya domin shawo kan matsalar tsaro a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hare-hare a sassa daban-daban na garin, inda suka addabi mazauna tare da jikkata mutane da dama, yayin da aka kuma samu asarar rayuka a wasu wurare.
Yayin rikicin wani matashi ya rasa ransa bayan da aka kai masa hari a hanyar da ta nufi harabar jami’ar Jos, lamarin da ya kara tayar da hankalin jama’a.
Haka kuma wasu direbobi da ke zirga-zirga a yankunan Terminus, Bauchi Road da Gangare sun fuskanci farmaki, inda aka lalata motocinsu tare da fasa gilashi.
Wuraren da rikicin ya fi shafa sun hada da yankin jami’ar Jos, Farin Gada, mahaɗar Tina da Chobe, inda harkokin kasuwanci suka tsaya cak sakamakon fargabar tsaro.
Mazauna yankin sun bayyana cewa sun tsorata matuka, inda da dama suka rufe shagunan su tare da komawa gidajensu saboda tsoron abin da ka iya biyo baya.
Dokar hana fitar dai an sanya ta ne bayan wani mummunan hari da ya faru a Angwan Rukuba, inda aka samu asarar rayuka masu yawa sakamakon rikici tsakanin wasu matasa.
Jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji sun isa wuraren da lamarin ya shafa, inda suka fara daukar matakan kwantar da tarzoma tare da dawo da zaman lafiya.
Rahotanni sun nuna cewa bayan zuwan jami’an tsaron ne aka samu saukin tashin hankalin a wasu yankuna, duk da cewa har yanzu ana ci gaba da sanya ido domin hana sake barkewar rikici.













































