Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 3 ga watan Afrilu da kuma ranar Litinin 6 ga watan Afrilu na shekarar 2026 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Easter na wannan shekara.
Ranar 3 ga Afrilu ita ce Juma’a mai tsarki, yayin da ranar 6 ga Afrilu ita ce Easter Monday.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
Ya taya mabiya addinin Kirista a Najeriya da ma wadanda ke kasashen waje murnar wannan lokaci na Easter.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi tunani a kan kyawawan dabi’u da ke tattare da wannan lokaci, inda ya jaddada muhimmancin sadaukarwa, yafiya, hakuri da kauna kamar yadda rayuwa da koyarwar Yesu Almasihu suka nuna.
Haka kuma ya yi kira ga hadin kai tsakanin ‘yan kasa, da muhimmancin zaman lafiya da juna domin cigaban kasa.
Ministan ya kara da cewa wannan lokaci na Easter yana tunatar da al’umma muhimmancin hakuri da zama tare cikin fahimta, wanda ke taimakawa wajen karfafa hadin kan kasa.
Ya kuma bayyana kudurin gwamnatin tarayya na aiwatar da manufofi da za su kawo cigaban kasa, bunkasar tattalin arziki da walwalar ‘yan Najeriya baki daya.
Ya yi wa mabiya addinin Kirista fatan yin bikin Easter cikin lumana da farin ciki.













































