Tinubu ya sabunta naɗin Bugaje a matsayin shugaban hukumar NBTE

Professor Idris Bugaje 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sabunta naɗin Farfesa Idris Bugaje a matsayin sakataren zartarwa na Hukumar kula da ilimin fasaha ta ƙasa (NBTE).

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Mista Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba a Abuja.

Sabon naɗin ya ba Bugaje damar fara wa’adi na biyu kuma na ƙarshe na shekaru biyar bayan kammala wa’adinsa na farko.

An fara naɗa Bugaje a matsayin sakataren zartarwa na NBTE a ranar 14 ga Maris, 2021, na wa’adi na farko na shekaru biyar.

Tinubu ya amince da sabunta naɗin ne bayan nazarin aikinsa, jagoranci, da gudunmawar da ya bayar wajen sauya fasalin ɓangaren ilimin sana’o’i da koyon aiki (TVET).

Sanarwar ta bayyana cewa an samu ci gaba mai yawa wajen inganta tsarin TVET a Najeriya ƙarƙashin jagorancin Bugaje.

Hukumar NBTE ta gudanar da gyaran tsarin manhajoji gaba ɗaya domin daidaita ilimin fasaha da buƙatun ƙwarewar duniya.

Haka kuma, hukumar ta ƙirƙira da kuma sake duba kusan manhajoji na ƙasa guda 100 da suka dace da canjin buƙatun masana’antu da kasuwar aiki.

Sanarwar ta bayyana cewa waɗannan gyare-gyaren sun yi daidai da manufofin gwamnatin na farfaɗo da ilimi.

Tinubu ya buƙaci Bugaje da ya ƙarfafa gyare-gyaren da ake yi tare da tabbatar da kammala muhimman shirye-shirye da ake gudanarwa.

Shugaban ƙasar ya nuna ƙwarin gwiwa cewa wa’adi na biyu zai ƙara bunƙasa ilimin fasaha da haɓaka ƙwarewar aiki a faɗin ƙasar.

Ana sa ran wannan sabunta naɗin zai taimaka wajen ci gaba da ƙarfafa ci gaban ma’aikata da bunƙasar masana’antu a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here