Hukumar FRSC ta yi sauyin wurin aiki ga jami’ai 162, ta nada sabon mai magana da yawunta

FRSC Shehu Mohammed sabo 750x430

Shugaban hukumar kiyaye haduwa ta kasa FRSC Malam Shehu Mohammed, ya amince da sauya wurin aiki ga manyan jami’ai 162 a wani babban sauyi da aka yi a manyan mukaman hukumar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakin kwamandan runduna mai kula da gudanarwa, Mista Agboola Olundegun, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.

Mohammed ya bayyana cewa an yi wannan sauyin ne domin karfafa ayyuka da kuma inganta tsaron hanyoyi a fadin kasa.

Ya ce wannan tsarin ya hada da nadin sabbin kwamandojin yankuna guda hudu da kuma sauya wurin aiki ga kwamandojin sassa zuwa muhimman jihohi da sassan aiki a duk fadin kasar.

Shugaban hukumar ya kuma amince da nadin sabon shugaban sashen wayar da kan jama’a, inda aka daga mukamin tsohon mataimakin shugaban sashen, Osondu Ohaeri, domin jagorantar harkokin sadarwa da jama’a na hukumar.

Sanarwar ta ce jihohin da abin ya shafa sun hada da babban birnin tarayya Abuja, Rivers, Kaduna, Bauchi, Imo, Benue, Yobe, Ogun, Delta, Osun, Kogi, Bayelsa da Akwa Ibom.

Haka kuma an nada sabbin kwamandojin yankuna da suka hada da C.Z. Mathew (Benin), A.L.O. Ruk (Enugu), B.S. Akande (Sokoto) da Leye Adegboyega (Bauchi).

A gefe guda kuma, an mayar da wasu kwamandojin runduna zuwa mukaman kwamandojin sassa domin karfafa ayyukan a fili a jihohi daban-daban.

Daga cikin su akwai AP Longkam (Kaduna), O. Ogunjobi (Ogun), VA Kayode-Oni (Benue), PE Bedford (Edo), CE Edem (Delta), FA Ajatta (Rivers), FM Kalu (Akwa Ibom), SO Ordu (Bayelsa) da T. Iliyasu (babban birnin tarayya Abuja).

Sauran sun hada da KB Kazeem (Kwara), LL Fagge (Kogi), ON Okoro (Imo), ST Adebayo (Osun), SD Kehinde (Oyo), I Baba (Yobe) da CS Luka (Bauchi).

Mohammed ya ce an yi wannan sauye-sauyen ne bisa kwarewa, tarihin aiki da kuma bukatun hidimar kasa.

Ya kara da cewa hukumar na da kudurin sanya mafi kyawun jami’anta a wuraren da za su fi tasiri wajen gudanar da aiki.

Shugaban hukumar ya bukaci sabbin jami’an da aka nada su nuna kwarewa, sabuwar himma da kuma nagartaccen jagoranci a ayyukansu.

Haka kuma ya sake jaddada manufar hukumar na rashin juriya ga karya dokokin hanya da kuma hadurran da za a iya kaucewa a fadin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here