Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin bankin abinci na kasa

Minister of Agriculture Sen Abubakar Kyari 750x430

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani shirin bankin abinci na kasa da ya dogara da al’umma domin karfafa tsaron abinci da kuma fadada damar samun abinci mai gina jiki ga ‘yan Najeriya masu rauni a fadin kasa, musamman gidajen da ke fuskantar yunwa da matsalar karancin abinci mai gina jiki.

Shirin wanda ofishin matar shugaban kasa karkashin jagorancin Oluremi Tinubu ya jagoranta, yana da nufin kai tallafin abinci ga gidaje masu bukata musamman mata da yara, ta hanyar tsarin rarraba abinci da ya hada da hadin kan al’umma.

Ministan noma da tsaron abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana shirin a matsayin wata muhimmiyar hanya ta sauya daga tallafin gaggawa na abinci zuwa tsarin kasa mai dorewa da aka tsara yadda ya kamata.

Kyari ya bayyana haka ne yayin kaddamar da shirin a ranar Alhamis a Abuja, inda ya ce miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da rashin samun isasshen abinci mai gina jiki, musamman yara ‘yan kasa da shekaru biyar da abin ya fi shafa.

Ya ce an gina shirin ne bisa tsarin al’umma mai karfi da kuma hadin kai na kasa domin tabbatar da cewa tallafin ya kasance cikin tsari, gaskiya da dorewa, tare da inganta yadda ake kai abincin da aka noma a gida ga masu bukata.

Ya kuma jaddada cewa shirin ya kunshi hadin gwiwar bangarori da dama, inda ya yaba da rawar da Bankin Noma ke takawa wajen hada abinci da kuma rarraba shi zuwa al’umma domin rage asarar bayan girbi da kara tasiri a kasa baki daya.

Daya daga cikin mambobin kungiyar yaki da matsalar rashin abinci mai gina jiki ta duniya, Dakta Mansur Mukhtar, ya bayyana shirin a matsayin wani babban mataki wajen yaki da yunwa da karancin abinci mai gina jiki a Najeriya.

Mukhtar ya yabawa ofishin matar shugaban kasa bisa kirkiro da wannan shiri wanda ya hada tausayi, shugabanci da tsari mai kyau domin tallafawa masu bukata a fadin kasa.

Ya kuma yi kira ga hukumomin gwamnati, kungiyoyin farar hula, bangaren masu zaman kansu da abokan hulda na kasa da kasa da su hada kai domin tabbatar da nasarar shirin a nan gaba.

Ya kara da cewa tsaron abinci ba kawai bukatar jin kai ba ce, har ma yana da muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziki, zaman lafiya da ci gaban kasa.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya nuna cewa shirin na nufin sauya tsarin bayar da agajin gaggawa zuwa tsarin da ya fi tsari da dorewa wajen tallafawa masu bukata.

Ta hanyar hada samar da abinci, tarawa da rarrabawa tare da hadin kan al’umma, ana sa ran shirin zai rage matsalar rashin abinci mai gina jiki da kuma tabbatar da samun abinci mai inganci ga ‘yan Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here