A karon ƙarshe, shugabannin APC karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ana sa ran za su ziyarci tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a ranar Talata mai zuwa a Kano.
Wata majiya mai tushe daga sakatariyar APC ta ƙasa ta bayyana wa jaridar Solacebase cewa an kammala shirye-shirye domin kai ziyarar tare da roƙon Malam Ibrahim Shekarau da ya koma APC domin ƙarfafa jam’iyyar a jihar da ma ƙasa baki ɗaya, inda tsohon sanatan Kano ta tsakiya ke da dimbin magoya baya.
Malam Ibrahim Shekarau, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP, shi ne ya jagoranci yakin neman zaɓen Atiku Abubakar a jihar Kano a zaɓen shekarar 2023.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa majiyar ta ƙara da cewa an riga an fara tuntubar masu ruwa da tsaki na tsohon gwamnan domin sauƙaƙa yiwuwar sauya sheƙa.
Wannan mataki ana kallonsa a matsayin wata hanya ce da APC ke ƙoƙarin ƙarfafa tasirinta a Kano gabanin zaɓen 2027, musamman bayan sauya sheƙar gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf, daga NNPP zuwa APC.
Hakazalika, jagoran ƙungiyar Kwankwasiyya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sauya sheƙa zuwa ADC a ranar Litinin.












































