Wani malami ya asirce abokinsa dake Amurka tare da ƙwace masa kuɗaɗe da iyali

'Yan sanda sun kama wata mata da ake zargin ta kashe mijinta, ta jefar da gawar a wani kango
'Yan sanda sun kama wata mata da ake zargin ta kashe mijinta, ta jefar da gawar a wani kango

An kama wani malami mazaunin Legas, Alhaji Afeez Imoleayo, bisa zargin yi wa abokinsa da ke zaune a Amurka asiri tare da sace masa Naira miliyan 105 sannan ya ƙwace masa mata da ƴaƴa .

Mataimakin Sufeto-Janar na ƴansanda, AIG, na shiyya-2, Mista Ali Mohammed, ya gabatar da wanda ake zargin tare da wasu mutane biyar da suka hada da Ramon Uthman, Saidi Ajayi, Alhaja Monsurat Salami da Kikelomo.

AIG ya ce malamin ya kuma yi wa matar abokinsa da ƴaƴansa uku asiri ya dauke su a matsayin nasa.

Mohammed ya ce baya ga kudi iyalin abokin, malamin da matarsa ​​sun kuma kwace motoci biyar tare da ƙwace masa kadarorin gidaje da filaye.

Ya shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa da cewa ya yi amfani da asiri wajen kwace iyalan abokinsa, da kuɗaɗe sama da Naira miliyan 105 da wasu kadarorin da ya sauka a Legas.

Ya ce malamin ya amince cewa ya yi wa abokin sihirin ne ya canza sunayen ‘ya’yansa da takardun fili zuwa nasa.

A cewar Mohammed, wani dan Najeriya mai suna Animashaun ne ya shigar da kara gaban ‘yansanda a ranar 17 ga watan Yulin 2023, wanda ya kai ga kama malamin da matarsa.

Ya kara da cewa a halin yanzu akwai sauran wadanda suka hada baki da malamin da matarsa, amma sun gudu, sai dai kuma an kama mutane biyar bisa laifin aikata laifin.

Ya kuma ce an kwato farar mota kirar Toyota Venza 2009 guda daya, Ashok Leyland Bus daya da kadarori daban-daban daga hannun wadanda ake zargin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here