Hukumar yaki da masu yi wa tattalin Arziki tu’annati (EFCC) shiyyar Ilorin, ta gurfanar da wasu jami’an hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kwara (SUBEB) su shida a gaban mai shari’a Akanbi na babbar kotun jihar da ke zaune a Ilorin bisa zargin zamba.
A cewar wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na hukumar yaki da cin hanci da rashawa Dele Oyewale, ya fitar, ya ce jami’an SUBEB na fuskantar tuhume-tuhume hudu da suka hada da zamba cikin aminci da almubazzaranci da kudaden da suka kai Naira miliyan 96.
Wadanda ake tuhumar su ne Ahmed Husain Olarewaju, Daraktan Kudi da samar da kayayyaki da Omole Omololu John, mai kula da harkokin kudi da asusu, da Fatai Oyerinde, jami’in Sashen Albashi, sai Mujeeb Ibrahim babban jami’in kula da lissafin kudi da jadawalin albashi da Salami Temitope Bashir da Dauda Aweda Quozim, dukkansu ma’aikatan Sashen Albashi da ke SUBEB a jihar Kwara
Karin karatu: Zambar Naira Biliyan 1.96: Don Allah a ba ni damar tattaunawa da EFCC – Tsohon Akanta ya roki kotu
Wadanda ake zargin sun hada baki ne tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020 wajen canza kudaden jama’a mallakar gwamnatin jihar Kwara domin amfanin kansu tare da raba abin da aka samu a tsakaninsu.
Sai dai dukkannin su sun musanta zarge zargen da ake yi musu.
Mai shari’a Akanbi ya dage sauraren karar har zuwa ranar Laraba 16 ga Afrilu, 2025 tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali da ke Ilorin.