Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya ce a halin yanzu gwamnatin jihar tana daukar nauyin dalibai kimanin 2,600 da ke karatu a jami’o’i daban-daban, a kasashe 14.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a wajen bude taron baje kolin kungiyar EU karo na farko a nahiyar Afirka, a Afficent Event Centre dake Kano.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta hada gwiwa da masu ruwa da tsaki, ciki har da kasashen Turai don kara bude kofa ga jama’ar jihar.