Kotun Koli Ta Bawa Yan Najeriya Kunya Bisa Goyon Bayan Nasarar Tinubu – PDP

tinubu and atiku.jpeg
tinubu and atiku.jpeg

Jam’iyyar PDP ta bayyana kaduwarta game da hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

PDP, a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan hukuncin kotun kolin, ta lura da cewa “hakika yawancin ‘yan Najeriya sun firgita, kuma sun damu matuka da hujjar kotun koli da PDP ke ganin ya sabawa kayyadadden tanadin kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.”

Jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa hukuncin wani sharhi ne mai ban tausayi ga dimokuradiyyar Najeriya, inda ta yi zargin cewa kotun koli ta kasa tabbatar da tanade-tanaden dokar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here