Majalisar tarayya a ranar Alhamis ta amince da buqatar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, na gyaran kundun gudanarwa na 2022.
Hakan ya biyo bayan buqatar kashewa ‘yan kasa adadin kudin daya kai dalar amurka miliyan 800, domin rage radadin tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar baki daya, bayan cire tallafin man fetur.
Gyaran kundin gudanarwar ya tsallake zama na farko, na biyu har ma da na uku, a majalisar, biyo bayan zaman da majalisar ta gudanar ranar laraba.
Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewar, hakan ya faru ne a kasa da awa ashirin da hudu, bayan karanta wasikar shugaban kasar a ranar Larabar.













































