Gwamnan jihar Barno, Babagana Umara Zulum, ya amunci da nadin tsohon ministan noma da kiwo, Malam Bukar Tijani a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar ta Barno.
Gwamnan na Barno, ya sake nada Farfesa Isa Hussaini Marte a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar.
Sanawar nadin nasu na kunshe wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin jihar Malam Isa Gusau, ya fitar a ranar Laraba.
A cikin sanarwar Zulum ya bayyana Tijani a matsayin mutumin dake da karewa tare da gogewa la’akari da manya-manyan mukamen da ya rike wadan da suka hada da mukamin minista da sauran su.













































