Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya yi bayani kan rahoton faduwar layin rarraba wuta na kasa da ya faru a ranar Asabar, yana mai bayyana lamarin a matsayin “matsalar wucin gadi.”
Faduwar layin wutar da ta faru da safe a ranar Asabar ita ce karo na uku a wannan makon, inda jihohi da dama suka shiga cikin duhu.
Hakazalika wannan shi ne karo na takwas da aka samu irin wannan matsala a shekarar 2024.
Mai magana da yawun TCN, Ndidi Mbah, ya tabbatar da cewa an mayar da wutar lantarki, yana mai bayanin cewa matsalar ta samo asali ne daga fashewar wani sashin na’urar canza wuta a tashar rarraba wuta ta 330kV da ke Jebba.
“Na’urar kariya ta dauki mataki nan take, inda ta raba sassan layin wutan don guje wa lalacewar kayan aiki da kuma tashin gobara,” inji Mbah.
Injiniyoyin da ke tashar Jebba sun yi nasarar ware na’urar da ta lalace, sannan sun sake tsara hanyar rarraba wutan, wanda ya ba da damar dawowa da wutar lantarki a tashar da sauran sassan layin rarraba wuta na kasa.