Hukumar Alhazai zata fara jigilar alhazan Najeriya daga Saudiyya

NAHCON 1 2

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta ce jigilar alhazan Najeriya daga Saudiyya za ta fara daga ranar Laraba.

Hukumar ta bukaci alhazan da za su dawo su bi ka’idojin kayayyaki da takardu domin guje wa jinkiri.

Shugaban Sashen Sufurin Jiragen Sama na NAHCON, Alhaji Habib Bello, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Makka.

Bello ya ce kamfanonin jiragen sama da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) ne ke tsara jadawalin zirga-zirga kuma take amincewa da shi, wadda ke ba wa dukkan kamfanoni damar tashi.

A cewarsa, Max Air zai fara jigilar dawowar a ranar 3 ga Yuni da alhazan Jihar Nasarawa, yayin da Flynas da Air Peace za su fara aiki a ranar 4 ga Yuni da alhazan Jihohin Ogun da Oyo.

Ya bukaci alhazai da su bi dukkanin ka’idojin kayayayyakinsu da aka amince da su na jakunkuna biyu masu nauyin kilogiram 23 kowanne da jaka daya ta hannu mai nauyin kilogiram 8.

“Rashin bin ka’ida na iya haifar da jinkiri ko cire suna alhaji daga jerin fasinjoji.

“Haka nan alhazai suna bukatar sanar da jami’ai akalla sa’o’i 48 kafin tashi domin saukaka fitar da fasfo, shirya kaya da tsara tafiyar,” in ji shi.

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Fasfo na Makka, Alhaji Abdurrahman Mohammed, ya ce hukumar ta kammala mataki na farko na aikin Hajjin shekarar 2026 cikin nasara kuma sun fara tsara fasfunan alhazai da za su dawo.

Mohammed ya ce an ajiye fasfunan cikin amintaccen wuri domin gudun bacewa, lalacewa da guduwa, inda ya kara da cewa alhazai dole ne su mika bayanansu na tafiya akalla sa’o’i 48 kafin tashi domin yin aiki ba tare da matsala ba.

Ya ce an samar da hanyoyin da za a bi wajen dawo da fasfunan da suka bace ko a ba da Takardar Tafiya ta Gaggawa idan ya cancanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here