Miji da mata sun tsallake rijiya da baya yayin da kwantena ta fado kan motarsu kirar Lexus Jeep a Toyota bus stop, kan titin Apapa-Oshodi, Lagos.
Daraktar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Lagos, Margaret Adeseye, ta ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 6:35 na yamma ranar Laraba, yayin da daya daga cikin kwantenan tirela ta fado kan bayan motar.
Jami’an kashe gobara sun ceto mutanen biyu ba tare da rauni ba, tare da taimakon jama’a da suka fara kai dauki kafin zuwansu.
An kuma tabbatar da lafiyar direban tirelar.
Hukumar LASEMA da LASTMA sun gyara hanyar da abin ya faru, yayin da ‘yan sanda daga ofishin Ilasamaja suka tabbatar da zaman lafiya a wurin.












































