Tsohon Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa, Barrister Hudu Yunusa Ari, ya roki Babbar Kotun Jihar Adamawa da ta dakatar da shari’arsa har sai Kotun Daukaka Kara da ke Yola ta yanke hukunci kan karar da ya shigar.
Lauyan Jihar, Chief L. D. Nzadon, ya yi watsi da rokon Ari, yana mai cewa hakan ya saba wa dokar shari’ar laifuka, kuma ya bukaci kotu ta yi watsi da bukatar.
Alkalin kotun, Justice Benjamin Manji Lawan, ya dage sauraron shari’ar zuwa 30 ga Janairu, 2025, don yanke hukunci kan bukatar Ari.
Ari yana fuskantar shari’a ne kan ayyana sakamakon zaben gwamna na 2023 ba tare da kammala tattara sakamako ba, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.
Wannan ya sa aka dakatar da shi daga mukaminsa a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.