Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Sakkwato ta gargadi mambobinta da su gujewa tsarin yin amfani da su wajen kalaman batanci domin samun tagomashi daga ‘yan siyasa.
Majalisar ta yi wannan kirane a cikin wata sanarwar da ta fitar a karshen taronta na Majalisar wanda Shugaban NUJ na jiha da Sakatariyarsa Dalhatu Safial-Magori da Muhammad Bello suka sanya wa hannu.
“Yayin da babban zabukan 2023 ke kara gabatowa kamata yayi mambobin mu su ci gaba da kasancewa maaikata abjin koyi tare da tabbatar da amincewar jama’a ta hanyar tabbatar da gaskiya da yin aiki cikin kwarewa.
Majalisar ta kuma yi kira ga ‘yan siyasa da su tabbatar sun gudanar da aikin zabe cikin lumana kafin zabe da lokacin da kuma bayan zabe.
Daga nan sai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar Sokoto da su kara samar da hanyoyin da za a bi wajen magance matsalolin tsaro da suka addabi jihar da ma kasa baki daya.
Majalisar ta kuma yi kira ga wadanda suka cancanci kada kuri’a da suka yi rajista amma har yanzu ba su karbi katin zabe na dindindin ba da su yi hakan, domin gudun kada a sha su basilla.
Kungiyar daganan ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta kwashe tarkacen sharar da ke cikin kasuwar Abu Dankure tare da cike ramukan da ke duk wata hanya da ke cikin birnin.
Ta kuma yabawa gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Sokoto da kuma hukumomin tsaro bisa namijin kokarin da suke yi na magance matsalolin tsaro dasuka addabi jihar. (NAN)













































