Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a da aka samu a zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Jihar Kano na iya kasancewa sakamakon watan Ramadan da kuma yadda jama’a suka ɗauki zaɓen a matsayin wanda ya shafi ’yan takara kaɗan.
Kwamishinan Zaɓe na Jihar Kano, Ambasada Abdu Zango, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a lokacin da yake duba yadda zaɓen ke gudana a Ƙaramar Hukumar birnin Kano.
Ya bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin lumana ba tare da tashin hankali ba, yana mai yaba wa mazauna jihar kan yadda suka nuna halin kirki.
A cewarsa, babu wata matsalar tsaro da aka samu, kuma babu barazana a bayyane ko a ɓoye.
Dangane da dalilin da ya sa wasu jam’iyyun adawa ba su shiga zaɓen ba, ya ce hukumar ba ta samu wata ƙorafi ko tuhuma ba.
Ya ƙara da cewa ba aikin hukumar ba ne zaɓar wanda zai shiga zaɓe, domin duk jam’iyyar da ta gudanar da zaɓen fidda gwani tare da cika sharuddan Dokar Zaɓe, za a amince da ɗan takararta.
A cewarsa, shawarar shiga ko rashin shiga zaɓe alhakin jam’iyyun siyasa ne.













































