Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta ce ta bibiyi ayyukan gwamnatin tarayya guda 35 da darajarsu ta kai Naira Biliyan 4.61 a Jihar Zamfara.
Shugaban tawagar bibiyar ayyukan, Dakta Murtala Bankano, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Gusau ranar Asabar.
Ya ce manufar shirin ita ce tabbatar da an samu ƙimar kuɗi bisa kuɗin da aka kashe tare da bibiyar Ayyukan Mazabu da na Zartarwa (CEPTI) haɗin gwiwa da Ofishin Kasafin Kuɗi.
Ya ƙara da cewa sauran abokan hulɗar sun haɗa da Cibiyar Ƙwararrun Masu Kimanta Gini ta Ƙasa (NIQS), kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ingantaccen aiwatar da ayyukan gwamnatin tarayya a faɗin ƙasa.
Ya ce ayyukan da aka bibiya a zagaye na takwas a jihar sun shafi fannoni shida da suka haɗa da ilimi, lafiya, albarkatun ruwa, wutar lantarki, tallafawa jama’a da noma.
A cewarsa, wasu ayyukan suna kan matakai daban-daban na kammalawa, don haka ya buƙaci ’yan kwangila da su koma wuraren ayyukansu domin yin abin da ya dace.
Bankano ya ce burin ICPC a ƙarƙashin wannan shiri shi ne tabbatar da an aiwatar da ayyukan mazabu da na zartarwa yadda ya dace bisa ƙa’ida.













































