Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu Sakkwato, ya kafa kwamitin mutane 19 domin sake duba gwanjon kayan gwamnati da tsohuwar gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta yi, kan zargin saba ka’ida.
Gwamnan ya dora wa kwamitin alhakin duba dukkan gwanjon kayan gwamnati da tsohuwar gwamnatin ta yi ba bisa ka’ida ba, domin gadara da kusanci.
Kwamitin zai kasance ne karkashin jagorancin Alhaji Jelani Kalgo da kuma Mustapha Alkali, Sakatare.
Sauran mambobin sun hada da Kanar Garba Moyi, Hon. Isah Sadik Achida, Dalhatu Sidi Mamman, Alhaji Harande Mahe, Hon. Nasiru Shehu Bodinga, Alhaji Mu’azu Suleiman, Alhaji Sanusi Danfulani, Alhaji Ibrahim Hassan, Alhaji Isah Mai Shinkafa, Alhaji Nasiru Manjo da Abubakar Salame.
Sauran su ne wakili daga ma’aikatar ayukka da ta kananan hukumomin jiha, da wakilin hukumar safiyo ta jiha, da wakili rundunar ’yan sandan jiha, da wakilin hukumar tsaro ta DSS da kuma sibil difens.
An zargi Tambuwal da yi wa kansa gwanjon motocin alfarma da kuma yi wa kwamishinoninsa da kantomomin kananan hukumomi 23 gwanjon motoci.