Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa kwamitin shirin ciyar da jama’a na watan Ramadan na shekarar 2026/1447AH domin sa ido kan rabon abinci ga mazauna jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, yace an ce an fara rabon abincin tun ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026, a cibiyoyi 115 da ke ƙananan hukumomi takwas na birnin Kano.
Gwamnan ya bayyana cewa shirin na da nufin tallafa wa marasa galihu tare da rage wa al’umma wahalhalun azumin watan Ramadan.
Ya buƙaci mambobin kwamitin da su gudanar da aikinsu cikin jajircewa, gaskiya da riƙon amana domin tabbatar da nasarar shirin.
Jaridar Solacebase ta yawaito cewa Kwamishinan Ma’aikatar Harkokin Addini, Ahmed Tijani Auwalu, shi ne shugaban kwamitin.
Sauran mambobin sun haɗa da kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman daga ma’aikatu daban-daban, shugabannin ƙananan hukumomi a yankin birnin Kano, da manyan jami’an Gidan Gwamnati.
Gwamnan ya jaddada cewa shirin ciyar da jama’a na Ramadan na daga cikin muhimman tsare-tsaren jin ƙai na gwamnatinsa domin ƙarfafa haɗin kai da tallafa wa al’umma masu buƙata a faɗin Jihar Kano.













































