Kamfanin sufurin jiragen sama na Azman Air ya sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragensa a fadin kasar har Illa masha Allah.
Hakan dai ya yi daidai da umarnin da kungiyar mamallaka Jiragen Sama ta Najeriya AON ta bayar na dakatar ayyukanta sakamakon tashin man jirgin da ake fama da shi a yanzu.
Sai dai kamfanin Ibom Air wanda gudana ne daga cikin mambobin kungiyar, ya ce zai ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda aka saba.
Kamfanin dai na Azman mallakin shugaban kungiyar AON ne Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina, wanda shi ne ya yi wa manema labarai karin haske kan batun tafiya yajin aikin tun ranar Juma’a.









































