Kamfanin sufurin jiragen sama na Ibom Airlines, yace ba zai dakatar da ayyukansa ba, kamar yadda kungiyar Mamallaka jiragen sama ta Najeriya AON ta sanar da tafiya yajin aiki a ranar Litinin.
Kungiyar ta AON dai a ranar juma’a ne ta sanar da tafiya yajin aikin sakamakon tashin farashin man jirgin sama zuwa Naira dari 700 kan ko wacce lita.
Ta cikin wata sanarwa da shugaban Kamfanin Mfon Udom, ya fitar ranar Asabar a Lagos, yace ya zama wajibi a sanar da al’umma cewa kamfanin baya tare da wancan hukuncin na kungiyar.













































