An yi jana’izar shahararren jarumin Kannywood, Umar Malumfashi

87421da2b9602123
87421da2b9602123

A safiyar yau Laraba, 28 ga watan Satumba ne aka gudanar da jana’izar shahararren jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa, Umar Malumfashi, a jihar Kano.

Dandazon jama’a da manya-manyan jaruman masana’artan sun samu halartan jana’izar marigayin inda aka sada shi da gidansa na gaskiya.

Fitattun abokan marigayi Umar Malumfashi cikinsu har da Salisu T. Balarabe daya daga cikin daraktocin fitaccen fim din Kwana Casa’in, inda jarumin ya ci sunan Ka-fi-gwamna sun halarci jana’izar a Kano.

Daga cikin manyan abokan sana’ar marigayin da suka sallaci gawarsa harda Salisu T. Balarabe daya daga cikin daraktocin fitaccen fim din Kwana Casa’in, wanda a cikin fim din ne jarumin ya ci sunan Ka-fi-gwamna, BBC Hausa ta wallafa a Instagram.

Sauran manyan iyaye a masana’antar kamar su Tahir Fagge, Alhaji Hamisu Iyantama da Baba Sogiji duk sun halarci jana’izar abokin sana’ar tasu. A daren ranar Talata, 27 ga watan Satumba ne aka samu labarin mutuwar marigayin wanda ya taba masoya da dumbin masu son kallon fina-finansa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here