Majalisar zastarwa ta amince a kashe naira milyan 580 domin sayo motoci masu sulke

Buhari signs signs 1
Buhari signs signs 1

Majalisar Zartarwa ta tarayya ta amince da Naira miliyan 580 domin siyan motocin sulke guda hudu don yaki da miyagun kwayoyi ga Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Muggan Kwayoyi.

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen taron majalisar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ya ce: “A yau, ofishin babban mai shari’a na tarayya ya gabatar da wata takarda da ke karkashin kulawar ofishin babban mai shari’a, hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.

“Manufar takardar ita ce neman amincewar majalisar don bayar da kwangilar samar da motoci masu sulke na musamman guda 14 ga hukumar.”

“Kudin kwangilar yakai kusan samada milyan N580 wanda ya hada da karin harajin kashi 7.5 cikin 100.”

Ministan ya ce an dauki matakin sayo motocin masu sulke ne domin karfafawa da kuma kare rayukan ma’aikatan hukumar da suka yi aiki tukuru tare da samun sakamako mai ban sha’awa.

A cewarsa, tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na shekarar 2022 hukumar ta kama mutane 18,940 da ake zargi da aikata laifuka 2,904.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here