Fiye da ƴan Najeriya miliyan takwas sun kammala rajistar zaɓe ta Internet – INEC

INEC Registration 750x430

Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta sanar da cewa sama da ‘yan Najeriya miliyan takwas ne suka kammala rajistar zaɓe ta internet a ci gaba da ake yi na rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasa.

A bayanin da hukumar ta fitar a Abuja, ta bayyana cewa mutane sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai ne suka kammala cikakken tsarin rajistarsu ta Internet da kuma daukar bayanai a wuraren da aka ware.

Rahoton ya nuna cewa jihar Imo ce ta fi kowace jiha yawan masu rajista da fiye da dubu ɗari takwas da ashirin da shida, wato kashi 10.32 cikin ɗari, sai Legas mai dubu 604, sannan Ogun da ta samu fiye da dubu 510.

Jihar da ta fi ƙaranci ita ce Yobe, da rajistar mutum 2,714 kacal, yayin da aka dakatar da aikin a Anambra saboda zaɓen gwamna da ke tafe.

Kididdigar hukumar ta nuna cewa mata sun fi maza yawan masu rajista da kashi 52.37 cikin ɗari, inda matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 suka mamaye da kashi 69.14 cikin ɗari.

Dalibai ne suka fi yawa a cikin masu rajista da kashi 25.23 cikin ɗari, sai ‘yan kasuwa da kashi 20.74, yayin da masu buƙata ta musamman suka kai 2.29 cikin ɗari.

Rahoton ya kuma nuna cewa jihohin Osun, Legas da babban birnin tarayya Abuja ne suka fi yawan waɗanda suka kammala rajistar gaba ɗaya, inda Osun ta samu fiye da mutum 151,000, Abuja mutum 106,000, sai Legas da mutum 85,000.

Hukumar ta bayyana cewa dukkan bayanan za su shiga tsarin tantancewa ta na’urar gano waɗanda suka yi rijistar fiye da ɗaya, sannan ta shawarci duk ‘yan ƙasa masu cancanta da su garzaya shafin internet na hukumar domin rajista.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here