Gwamnatin jihar Kebbi ta ba da umarnin a janye sarautun gargajiya da aka bayar ba bisa ka’ida ba

Idris

Gwamnatin Jihar Kebbi ta umarci dukkan majalisun masarautu, hakimai da shugabannin ƙauyuka da su dakatar da bayar da duk wata sarautar gargajiya ba tare da sahalewar ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da harkokin sarauta ta jihar ba.

Umarnin ya fito ne a cikin wata takarda da mataimakin daraktan gudanarwa na ma’aikatar, Abubakar Mansur-Tuga, ya sanya wa hannu, inda aka fitar da ita a Birnin Kebbi.

Takardar ta bayyana cewa an dauki matakin ne biyo bayan korafe-korafen da aka samu kan yadda ake bayar da wasu sarautun gargajiya ba tare da bin ƙa’idoji da dokokin da aka tanada ba.

Gwamnatin ta jaddada cewa dole ne bayar da sarautun gargajiya ya kiyaye mutunci, daraja da tsoffin al’adun da suka dade suna da nasaba da irin wadannan mukamai.

Ta kuma bayyana cewa a karkashin sauye-sauyen da ake aiwatarwa a halin yanzu, babu wata sarauta da za a bayar a kowane hali ba tare da samun amincewar ma’aikatar ba.

Haka kuma, takardar ta umurci a janye dukkan sarautun da aka bayar cikin watanni biyu da suka gabata wadanda ba su bi ka’idojin doka ba.

Haka kuma ta sanar da wadanda abin ya shafa nan take domin dawo da tsari da martabar tsarin bayar da sarautun gargajiya a jihar.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here