Ɗan majalisar wakilai daga Jihar Zamfara, Abdulmalik Zubairu na jam’iyyar APC, ya bai wa malamai addinin Musulunci 12 sababbin motocin Toyota Camry da darajarsu ta kai naira Miliyan 360 a jihar.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa Abdulmalik Zubairu na wakiltar mazabar tarayya ta Bungudu da Maru a majalisar wakilai ta ƙasa.
Daga cikin waɗanda suka amfana da kyautar akwai Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla, Sheikh Na’Allah Zurmi, Sheikh Usman Tambuwal, Sheikh Dr Atiku Zawiyya, Alhaji Yusuf Dinawa, Sheikh Abubakar Sodangi da Khalifa Ibrahim Zawiyya, tare da wasu malamai.
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ne ya miƙa motocin ga malamai a madadin ɗan majalisar, inda ya yaba da wannan mataki da ya ɗauka na tallafa wa malaman addini a jihar.
Gwamnan, wanda mai ba shi shawara na musamman kan harkokin addini, Malam Bello Almufty, ya wakilta, ya bayyana cewa wannan aiki alama ce ta cikakken wakilci, tare da jaddada muhimmancin girmama malaman addini ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.
A nasa bangaren, ɗan majalisar ya bayyana cewa kyautar na nuni da irin rawar da malaman addinin Musulunci ke takawa wajen yaɗa ilimin addini da wayar da kan al’umma kan zaman lafiya da gina ƙasa.
Kakakin dan majalisar Aminu Lawal, ya ce kowace mota an saye ta ne da kuɗi sama da naira miliyan 30, tare da kira ga malamai da su yi amfani da motocin yadda ya dace.
NAN











































