Ƙungiyar likitoci ta ƙasa NARD ta sanar da kudurin komawa yajin aiki na gaba ɗaya, mara wa’adi kuma cikakke, wanda aka sanya wa suna TICS 2.0, daga ranar 12 ga watan Janairu, 2026.
A makon da ya gabata, ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa ƙasar na iya fuskantar sake durƙushewar ayyukan kiwon lafiya a faɗin ƙasa, sakamakon gaza cika yarjejeniyar fahimta da gwamantin tarayya ta rattaba hannu da su a baya.
A cikin sanarwa da shugabanta, Dakta Mohammad Suleiman, ya fitar bayan taron gaggawa na kwamitin zartarwa na ƙasa, ƙungiyar ta bayyana cewa matakin na nufin matsa lamba kan gwamnati domin ta cika buƙatun da aka amince da su.
Ƙungiyar ta kuma sanar da shirye-shiryen gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya kan matsalolin walwalar likitoci, inda aka tsara zanga-zangar a asibitoci daban-daban a faɗin ƙasa daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Janairu, 2026.
NARD ta bayyana cewa, ta dauki matakin yajin aikin sakamakon gazawar ma’aikatar lafiya ta tarayya da gwamantin tarayya wajen bin jadawalin aiwatar da yarjejeniyar fahimta da aka cimma da likitocin horaswa, duk da wa’adin da aka bayar a lokuta da dama.
A matsayin shiri na komawar yajin aikin, an umurci shugabannin cibiyoyi 91 na ƙungiyar a faɗin ƙasa da su gudanar da tarukan majalisa tare da yi wa manema labarai bayani, domin jawo hankalin jama’a kan matsalolin walwalar likitoci.
Ƙungiyar ta ce dakatar da yajin aikin ba za a sake la’akari da shi ba sai an aiwatar da dukkan ƙananan buƙatunta, waɗanda suka haɗa da dawo da wasu likitoci da aka kora, biyan bashin albashi da karin girma, aiwatar da alawus na ƙwarewa gaba ɗaya, da warware matsalolin albashin likitocin koyon aiki, tare da kammala yarjejeniyar tattaunawar albashi cikin lokaci.













































