Fubara ne jagoran APC a jihar Rivers – Yilwatda

APC Yilwatda 682x430

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, shi ne ke jagorantar jam’iyyar APC a jihar.

Yilwatda ya faɗi hakan ne a yayin wani shiri mai suna Hard Copy da ake gabatarwa a gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, inda ya yi bayani kan tsarin jagoranci a jam’iyyar a matakin jiha.

Ya ce tsarin APC na bai wa gwamnoni damar jagorantar jam’iyya a jihohinsu, amma ya jaddada cewa dole ne a mutunta kowa tare da tabbatar da haɗin kai, ba tare da ware ko tauye haƙƙin sauran mambobin jam’iyyar ba.

Shugaban na APC ya ƙara da cewa aikinsa a matsayinsa na shugaban jam’iyya na ƙasa shi ne daidaita harkokin jam’iyya a matakin jiha, ba wai tilasta zaɓin shugabanci ko ɗaukar matakai ba tare da shawarwari ba.

Dangane da tambayar ko Siminalayi Fubara shi ne jagoran APC a Jihar Rivers, Yilwatda ya amsa da tabbatarwa, inda ya bayyana cewa wajibi ne gwamnan ya haɗa kai da sauran jiga-jigan jam’iyyar domin tafiyar da al’amura cikin tsari.

Game da yiwuwar goyon bayan Fubara idan ya nemi wa’adi na biyu, Yilwatda ya ce APC na bin tsarin zaɓen fidda gwani, kuma duk wanda ya fito a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ta hanyar zaɓen fidda gwani shi ne jam’iyyar za ta mara wa baya.

Ya bayyana cewa jam’iyya ba ta jingina goyon baya ga mutum ɗaya ba, sai dai ga duk wanda ya lashe zaɓen fidda gwani, inda ya ce hakan ne kaɗai zai tabbatar da adalci da dimokuraɗiyya a cikin APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here