Gwamnatin tarayya za ta dawo da ‘yan Najeriya 15,000 da suka makale a kasashen waje

Stranded Nigerians abroad 700x430 (1)

Gwamnatin tarayya ta ce ana ci gaba da tattaunawa kan yadda ‘yan Najeriya 15,000 da suka makale a kasashen Kamaru, Nijar, Chadi da sauran sassan duniya za a dawo da su Najeriya cikin aminci da mutunci.

Alhaji Tijani Ahmed, kwamishinan tarayya a hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure (NCFRMI), ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Juma’a a Abuja.

Ahmed ya bayyana cewa akalla mutane miliyan shida ne ke gudun hijira a Najeriya, yayin da dubban ‘yan gudun hijira ke zaune a wasu wurare a fadin duniya.

“Muna da ‘yan Najeriya 15,000 da ke son komawa kasar bisa radin kansu, haka nan muna da ‘yan kasashen waje da ba su gaza 100,000 da ke zaune a kasar nan a matsayin ‘yan gudun hijira.

Karin karatu: JAMB ta fitar da sakamakon UTME ta shekarar 2025

Yayin da yake nanata kokarin gwamnati na ganin an dawo da ‘yan gudun hijirar lafiya, Ahmed ya godewa shugaban kasa Bola Tinubu bisa goyon bayan da ake bai wa hukumar da ma’aikatar jin kai.

Shugaban NCFRMI ya kuma bayyana cewa Najeriya za ta karbi bakuncin taron jigo na farko a karkashin shugabancinta na Rabat Process, tare da wakilai sama da 100 daga kasashe 57 na hadin gwiwa.

Idan za a iya tunawa, Najeriya ta karbi shugabancin shirin Rabat – taron tattaunawa kan ci-rani da ci-gaban Yuro da Afirka – a watan Janairu, 2025.

Kwamishinan na tarayya ya kuma bayyana kalubalen da ake fuskanta wajen kula da tafiye-tafiye, ciki har da bukatar samar da isassun shawarwari don sanar da matasa hanyoyin yin hijira na doka.

“Yin hijira ba bisa ka’ida ba na iya haifar da wahala da haɗari, tare da yawancin bakin haure ba za su iya komawa ƙasarsu ta asali ba,” in ji shi.

Don haka Ahmed ya yi kira da a samar da ingantaccen hadin kai da goyon baya daga masu ruwa da tsaki, ciki har da kafafen yada labarai, don habaka tsarin tafiyar da bakin haure. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here