Lalata yunƙurin juyin Mulkin Benin: Barau ya yaba da rawar da Tinubu ya taka, ya ce dimokuradiyya ita ce mafi dacewa

WhatsApp Image 2025 12 08 at 14.50.23 750x430

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa kuma mataimakin shugaban majalisar dokoki ta kungiyar ECOWAS na farko, Sanata Barau I. Jibrin, ya yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa gaggauta amincewa da bukatar gwamantin Jamhuriyar Benin domin tura sojojin Nigeria su dakile yunƙurin juyin mulki da aka yi ƙoƙarin yi a kasar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, a ranar lahadi sojoji da suka bayyana kansu a matsayin kwamitin soja na tsarkakewa sun sanar da kifar da gwamnatin shugaban kasa patrice talon ta gidan talabijin na gwamnati.

Shiga tsakani na rundunar sojin Najeriya cikin hanzari ya taka muhimmiyar rawa wajen karya yunƙurin juyin mulkin tare da tabbatar da dawowar doka da oda a makwabciyar kasarta da abin ya faru.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai malam Ismail Mudashir ya fitar, Sanata Barau ya yaba wa shugaban kasa Tinubu bisa hanzarin da ya yi wajen amsa kiran Jamhuriyar Benin domin taimakawa wajen dakile rikicin.

Karanta: Yunkurin juyin mulki: Yadda Tinubu ya taimaka wajen kare Dimokuraɗiyyar ƙasar Benin – fadar shugaban ƙasa

Sanata Barau ya bayyana cewa dimokuraɗiyya ita ce tsarin mulki da yafi dacewa a wannan zamani, tare da jaddada cewa mulkin soja baya da gurbi a tsarin tafiyar da al’umma na duniya a yau.

Ya ce ta cikin majalisar dokoki ta kungiyar ECOWAS za a ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwar dokoki, raya dimokuraɗiyya, ƙarfafa haɗin kai na yankin da kuma faɗaɗa ci gaba da wadata a kasashen yammacin Afrika.

Sanata barau ya kara da cewa majalisar dokoki ta kungiyar ECOWAS na ci gaba da aikin gina tsayayyen yammacin Afrika ta hanyar karfafa diflomasiyyar majalisa, habaka hadin kai tsakanin kasashe mambobi da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro domin kare bunkasar yankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here