Mai shari’a Maryann Anenih na babbar kotun birnin tarayya Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.
Kotu ta amince da bada belinsa a kan kudi naira miliyan 500 tare da mutane biyu da za su tsaya masa a daidai wannan adadin, a ranar Alhamis.
Mai shari’a Anenih, a ranar 10 ga watan Disamba, ya ki amincewa da bukatar belin tsohon gwamnan, yana mai cewa an shigar da shi ne da wuri.
Kotun ta ki bayar da belinsa da farko bayan ta ce, “Bayan an shigar da wanda ake tuhuma na 1 ba a tsare ba, ko kuma a gaban kotu, bukatar nan take ba ta cika ba.
“Duk da haka akwai damar da lauyoyin gwamnan su shigar da sabon neman beli da kuma neman ranar sauraron karar.”
Tsohon gwamnan dai na fuskantar shari’ar karkatar da kudade har N110bn, tare da wasu mutane biyu.
Ya musanta aikata laifuka 16 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ke tuhumarsa da aikatawa.
A lokacin da aka bukaci a saurari karar, a ranar Alhamis, Lauyan Bello, Joseph Daudu, SAN, ya shaida wa kotun cewa lauyoyin masu kare wadanda ake kara sun shigar da kara a matsayin martani ga karar da lauyoyin masu gabatar da kara suka shigar.
Sai dai ya nemi a janye karan rantsuwar, yana mai cewa, “Ba ma so mu sanya lamarin ya zama rigima.”
Babu wata takaddama daga lauyan masu shigar da kara, Olukayode Enitan, SAN. Don haka kotun ta amince da bukatar janyewa, inda ta yi fatali da karin rantsuwar.