Masu satar bayanai sun yi wa shafi Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) kutse
Ofishin ya bayyana hakan ne a wani sakon da ta wallafa a shafinta na X (tsohon Twitter) a daren Laraba.
Sai dai ta ce ana ci gaba da kokarin dawo da shafin, inda ta gargadi ‘yan Najeriya da su yi watsi da duk wani sako ko rahoton da aka buga a shafin har sai an kwato shi.