Gwamnatin Osun ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin sanya guba a abincin wasu dalibai 18 a makarantar firamare ta St. James (B) Owoope da ke Osogbo.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kolapo Alimi ya fitar aka rabawa manema labarai ranar Talata a Osogbo.
Sanarwar ta ce Gwamna Ademola Adeleke shi ne ya ba da umarnin gudanar da binciken tare kuma da daina dafa abincin.
Sanarwar tace an gayyaci masu dafa abinci a makarantar da jami’in dake kula da su domin amsa tambayoyi a Talatar nan.
Karanta wannan:Kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya ya gyara wutar bayan da ta katse a ranar litinin
A cewar sanarwar, gwamnatin jihar ta biya duk wasu kudade na duba lafiyar daliban bayan an sallame su daga wani asibiti da ba a bayyana ba.
Shugaban Hukumar Ilimin bai daya na jihar, Mista Nathaniel Ojetola, ya ce an yi wa dalibai 18 jinya tare da sallamar su.